<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya Ruhun Allah, zo yanzu
 Ka sauko nan, ka cika mu.
 Ruhu mai shafewa ne kai,
 Mai ba da kyautar sabon rai.
 Sai dai ka ba mu kyautarka
 Da hasken rai da ƙaunarka.

[V2]
 2) Kullum ka ba mu haskenka
 Domin mu bi ka, Shugaba.
 Ka cika mu da murnarka,
 Ka haskaka fuskokinmu,
 Jaraba duk, ka kore ta,
 Inda ka ke, sai lafiya.

[V3]
 3) Kai Kyautar Allah, Ruhunsa,
 Mai koya mana sanin Ɗan,
 Ka nuna mana ƙaunarsa
 Domin mu riƙa yabonsa.
 Mu yi yabo ga Allahnmu
 Mai ba da haske da ƙauna.</lyrics>
<title>Ya Ruhun Allah, Zo Yanzu LW199</title>
<hymn_number>199</hymn_number>
</song>